Hukumar da ke kula da sufuri da kasuwancin man fetur a Najeriya ta bayar da sabbin lasisin shigo da man fetur daga ƙasashen ƙetare har guda 6, bayan tangarɗar da ake fuskanta ta samun wadatarsa a sassan ƙasar sanadiyar yaƙin da yanzu haka ke gudana a yankin Gabas ta tsakiya.
Hukumar ta ɗauki wannan matakin ne bayan da matatar Dangote ke fitar da man da ta ke tacewa zuwa ƙasashen ƙetare, a wani yanayi da farashinsa ke ci gaba da ƙaruwa a cikin Najeriya.
Najeriyar da ke sahun ƙasashen masu arziƙin man fetur ta ke kuma da matata mallakin attajirin Afrika Aliko Ɗangote da ke iya tace mai tare da sayarwa a gida da kuma fitarwa ƙetare, har yanzu al’ummarta na fama da matsananciyar matsalar ƙaranci da kuma tsadar mai.