Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke hukunci inda ta soke takardar shaidar cin zaɓe da Hukumar Zaɓe ta Kano (KANSIEC) ta bai wa shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso, Ghali Shitu Basaf.
Haka kuma, kotun ta ce a soke rantsuwar kama aikin da ya yi, lamarin da ya tayar da kura a siyasar yankin.
Wannan hukunci ya biyo bayan ƙarar da ɗan takara Ali Musa ‘Danmaliki ya shigar, inda ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka sauya sunansa a matsayin ɗan takara a lokacin zaɓen.
Lauyan Danmaliki, Barista Jazuli Mustapha, ya shaida wa manema labarai bayan kammala shari’ar cewa rantsar da Basaf ba ta bi ka’ida ba.
Ya ce matakin ya saɓa da dokokin zaɓe da kuma tsarin mulki.
Kotun ta umarci KANSIEC da ta ayyana Ali Musa Danmaliki a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso.