Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYan sanda sun yi artabu da masu kai hari a Kano yayin...

Yan sanda sun yi artabu da masu kai hari a Kano yayin farautar jagoran ‘yan bindiga

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta dakile wani hari da aka kai wa jami’anta yayin wani samame na kama wani da ake zargi da jagorantar ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Bichi.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar 22 ga Maris, bayan samun kiran gaggawa daga ofishin ‘yan sanda na Tudun Wulli.

A cewar majiyoyin, wata tawaga ta sashen yaƙi da garkuwa da mutane, ƙarƙashin jagorancin ASP Abubakar Musa, ta yi aiki da sahihan bayanan sirri inda ta bi sawun wani da ake zargi da jagorantar ‘yan bindiga mai suna Muhammad, wanda aka fi sani da “Senator” ko “Kirchi,” wanda ake zargin ya je ƙauyen Tudun Wulli domin bikin Sallah.

“An hango wanda ake zargin ne dauke da bindigar AK-47, amma yayin ƙoƙarin cafke shi, sai ya tsere cikin taron jama’a,” in ji majiyar.

Lamarin ya ƙara tsananta ne lokacin da wasu gungun jama’a suka kai wa jami’an ‘yan sandan hari da jifa da duwatsu da sauran makamai masu haɗari, lamarin da ya jikkata ASP Lawali Hamidu tare da lalata gilashin motar sintiri ta ‘yan sanda.

SourceZagazola
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments