Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiEFCC ta miƙa N387m da aka karkatar ga gwamnatin Jigawa

EFCC ta miƙa N387m da aka karkatar ga gwamnatin Jigawa

EFCC ta ce an kwato kudin su ne daga dukiyar jama’a da aka karkatar a baya

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta mayar wa gwamnatin Jihar Jigawa kudi har Naira miliyan 387 da ta kwato.

Hukumar ta bayyana cewa kudin na daga cikin dukiyar jama’a da aka karkatar ko aka yi amfani da su ba bisa ka’ida ba a baya.

Ta ce mayar da kudin wani bangare ne na kokarinta na tabbatar da cewa an dawo da kudaden da aka sace domin amfanin al’umma.

Jami’an EFCC sun ce an mika kudin ne bisa aikinta na yaƙi da rashawa da tabbatar da gaskiya da rikon amana. Sun kuma kara da cewa hakan na nuna yadda ake ci gaba da gano da kuma kwato kudaden da aka wawure a fadin kasa.

Gwamnatin Jigawa ta karbi kudin tare da nuna godiya ga EFCC kan wannan mataki.

Ta ce za a yi amfani da kudin wajen ayyukan da za su amfani al’ummar jihar.Hukumar EFCC ta kuma gargadi jami’an gwamnati da su guji aikata rashawa, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da bin diddigin duk wanda aka samu da laifi tare da kwato kudaden jama’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments