Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum guda bayan rikici tsakanin wasu kungiyoyin ‘yan daba a Kano.
Rahoton ya nuna cewa lamarin ya faru da misalin karfe 10.30 na dare a yankin Ja’en Unguwar Lalle, bayan wani taron sulhu tsakanin bangarorin ya ci tura.
Wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa wani mazaunin yankin ya kira yan sa ‘yan, inda sanda suka gaggauta isa wurin, suka shawo kan lamarin.
‘Yan sanda sun kama wasu shugabannin da ake zargi, daga xiki har da Abubakar Abdullahi mai shekaru 22 da Abubakar Bello wanda aka fi sani da Babuji mai shekaru 18.
Mutane uku sun samu munanan raunuka, inda aka kai su asibitin kwararru na Murtala Muhammad.
Daya daga cikinsu, Aliyu Abdullahi, ya rasu daga baya, yayin da sauran ke ci gaba da karbar magani.
Bincike na ci gabda gudana, inda ‘yan sanda suka sake kama wasu mutum takwas tare da kwato makamai irin su adda, takobi da kuma layu.