Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNNPC ya rage farashin man fetur a Lagos da Abuja

NNPC ya rage farashin man fetur a Lagos da Abuja

Kamfanin Man Fetur na Kasa, NNPC Limited, ya rage farashin man fetur a gidajen sayar da man sa, lamarin da ya kawo sauƙi ga masu ababen hawa a biranen Lagos da Abuja.

A gidajen sayar da man NNPC da ke Lagos, da suka hada da ciki har da Isheri Oshun Road, Apple Junction, da Ago Palace Way, yanzu ana sayar da litar man fetur kan Naira 1,130, daga tsohon farashin Naira 1,230.

A babban birnin tarayya Abuja, an rage farashin zuwa N1,165 kan lita a gidajen sayar da man da ke Jabi da Wuse, daga Naira 1,260 da ake sayarwa a baya.

Wannan ragin farashi ya biyo bayan da kamfanin ya rage N100 kan lita a jahar Lagos da kuma N95 a Abuja, duk da cewa wasu ‘yan kasuwar man fetur har yanzu ba su fara aiwatar da sabon ragin farashin da Matatar Dangote ta sanar ba.

Tun da farko, Matatar Dangote ta rage farashin man fetur da take sayarwa ga dillalai (gantry price) zuwa N1,075 kan lita, bayan da farashin danyen mai a kasuwar duniya ya sauka daga kusan $110 zuwa $88 kan ganga.

Masana sun danganta tashin farashin danyen mai a baya da tashin hankalin Gabas ta Tsakiya, musamman rikicin da ya shafi Amurka, Iran da Isra’ila, wanda ya haifar da fargabar tangardar samar da mai ko yiwuwar rufe Mashigar Hormuz (Strait of Hormuz).

Sai dai Kuma daga baya farashin ya fara sauka bayan Amurka ta nuna cewa rikicin na iya lafa, tare da tattaunawar ministocin kasashen Turai kan sakin wasu daga cikin ajiyar man fetur domin daidaita kasuwar duniya.

Haka kuma, Brent crude, wanda ake amfani da shi a matsayin ma’aunin farashin mai a duniya, ya sauka da kusan 8.45%, daga $110 zuwa kusan $92 kan ganga, abin da ya taimaka wajen rage farashin man fetur a cikin gida.s

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments