Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiEFCC ta kama wani sarkin gargajiya a Edo kan zargin zamba

EFCC ta kama wani sarkin gargajiya a Edo kan zargin zamba


Ofishin Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annaci (EFCC) na Benin ya kama wani sarkin gargajiya, HRM Michael Sado, wanda shi ne Okuokpellagbe na Okpella, a ƙaramar hukumar Etsako East ta Jihar Edo.

An kama sarkin tare da wani mutum mai suna Patrick Omkhagbo bisa zargin aikata damfara da wasu laifuffuka masu alaka da kuɗi.

An kama su ne biyo bayan ƙorafi da Majalisar Shugabannin Ƙauyukan Ukhomuyo ta shigar ga ofishin EFCC na Benin ta hannun lauyoyinsu A. O. Osagie & Associates.

A cikin ƙorafin, shugabannin ƙauyukan sun zargi sarkin da maida dukkanin al’ummar Ukhomuyio kamar kadararsa ta kansa. Sun kuma ce ya juya manyan kuɗaɗe da ake bai wa al’ummar daga albarkatun ƙasa na yankin zuwa asusunsa na kashin kansa.

Sun kuma zarge shi da rainawa al’umma hankali, Haka kuma sun ce ya karya yarjejeniyar ci gaban al’umma (Community Development Agreement – CDA) da ke tsakanin Okpella Cement Plc (Dangote Cement) da al’ummar Ukhumuniyo.

Shugabannin al’ummar sun bayyana cewa yarjejeniyar ta samo asali ne daga Sashe na 116 na Dokar Ma’adinai da Hakar Ma’adanai ta Najeriya ta shekarar 2007.

A cikin ƙorafin nasu sun ce:

“A cikin wannan yarjejeniyar CDA, an bayyana cewa al’ummar da ake hako ma’adinai a cikinsu wato Ukhumuniyo Community, inda kamfanin Okpella Cement Plc (Dangote Cement) ke gudanar da ayyukan hakar ma’adinai, za su rika karɓar wasu kuɗaɗe. An tanadi cewa za a rika biyan al’ummar Naira miliyan 250 a duk shekara.”

Sai dai sun ce ba tare da bin wannan yarjejeniya ba, sarkin ya buɗe wani sabon asusun banki da sunan Okpella Community Development, inda suka ce shi kaɗai ne mai sa hannu a asusun.

Sun ƙara da cewa suna ta roƙon matasa da sauran al’ummar Ukhomunyio kada su tayar da rikici, saboda wanda ake zargi yana barazanar haddasa rikicin cikin gida a al’ummar Okpella idan aka ci gaba da binciken zargin da ake masa, har ma kuma sun Kara da cewa, rashin tsaro ya riga ya zama ruwan dare a Okpella, don haka bai kamata a ɗauki barazanar da wasa ba.

Sun roƙi EFCC da ta kama, tare da gurfanar da waɗanda ake zargi, har da wasu ma’aikatan kamfanin simintin Dangote, domin a cewarsu ayyukan da ake zargi da su na ɗauke da alamu na manyan laifuffukan tattalin arziki kuma na iya haifar da rikici da rashin doka a cikin al’umma.


RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments