Najeriya ta yi gargaɗi kan haɗarin kamuwa da cutar sanƙarau a wasu jihohin Arewacin ƙasar.
Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya NiMet ce ta fitar da sanarwar gargaɗi game da lafiyar jama’a inda ta ce akwai jihohin Arewacin ƙasar da dama da ke fuskantar ƙarin haɗarin kamuwa da cutar sankarau yayin da yanayin zafi ke ƙaruwa a sassan ƙasar.
A cikin wata sanarwa, hukumar ta bayyana cewa cutar sanƙarau wata mummunar cuta ce da ke shafar ƙwayoyin kariya da ke rufe
ƙwaƙwalwa da lakar baya, kuma galibi ƙwayar cutar Neisseria meningitidis ce ke haddasa ta.
NiMet ta kuma bayyana cewa cutar na yaɗuwa ta hanyar numfashi daga mutum zuwa mutum, musamman a wuraren da ake cunkoso ko kuma wuraren da iska ba ta shiga yadda ya kamata.
Hukumar ta bayyana Sokoto, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Jigawa, Adamawa, Gombe, Bauchi, Yobe da Borno a matsayin jihohin da ke cikin babban haɗari na kamuwa da cutar.