Wasu manoman rani a Kano sun ce kokarinsu na wadata mutane da kayan abinci yana samun cikas.
A Agalawan Burji da ke karamar hukumar Madobi dake jihar kano, akwai manoman rani da ke kokarin shuka dankalin turawa.
Sai dai sun shaida wa ICONIC TIMES24 cewa akwai babbar matsala dake hana su wadata Kano da dankalin turawan.
Daya daga cikin Manoman, Yammani ya yi magana a madadin abokansa ya ce:
“Mun shuka dankalin turawa da karkashi da sauran kayan lambu, kamar su tumatur, albasa da alayyahu, mun fara shuka dankalin turawa mu gwada, ba mu samun irin dankalin turawa har sai an je garin Jos ake kawo mana”
ya kuma ƙara da cewa:
“Kalubalan da mu ke fuskanta shi ne babu hanyar mota da idan muka noma kayan, za mu fitar kasuwa.”
Ya buƙaci gwamnati ta yi ƙoƙarin a matso da nesa kusa domin a samun wadatar abinci a Kano da kewaye – da rani ko da damuna.