Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce bai kamata a bar gwamnatin Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar bayan harin haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila kan Iran, Netanyahu ya gode wa Amurka game da harin.
”Cikin shekara 47 gwamnatin Ayatollah na ambata mutuwa ga Isra’ila da mutuwa ga Amurka”, in ji shi.
”Gwamnatin Iran ta kashe ƴan Isra’ila da Amurkawa masu yawa, don haka bai kamata a bar wannan gwamnati ta malaki makamin nukiliya ba”, in Netanyahu.
Yana mai cewa harin da suka kai zai bai wa Iraniyawa damar ƙwace gwamnatinsu da hannunsu.