An kama mai tonon kabari a Jihar Gombe wanda ke tona kabari da kuma cirar sassan jikin mamaci.
Majiyoyi sun shaida cewa a ranar 24 ga watan Fabrairu, wani mai suna Zakari Ibrahim mai shekaru 45, dan kauyen Barwo Sabon Gari, ya bayar da rahoton cewa ya ga Umar Ibrahim mai shekaru 30 yana tona kabari.
Zakari Ibrahim ya ce Umar Ibrahim da ya kasance mazaunin unguwar Madaki a gundumar Barwo Winde, yana tona wani kabari a makabartar Barwo Sabon Gari.
Biyo bayan rahoton ne hukumomin yankin suka kama wanda ake zargi domin gudanar da cikakken bincike a kansa da daukar mataki.
Wanda ake zargi dai ya amsa laifinsa.
A yayin bincike, an ruwaito cewa Umar Ibrahim ya amsa laifin cewa mahaifinsa, Ibrahim Usman mai shekaru 60, ne ya aike shi domin cire wasu sassan gawar mamaci don amfani da su wajen tsafi.
Sai dai duk da amsa laifinsa, Umar Ibrahim bai bayyana hakikanin irin tsafin da suke yi da sassan gawa ba da kuma shekarun da ya shafe yana hakan.