Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya sauke Egbetokun daga mukamin Sufeton yan sandan Najeriya

Tinubu ya sauke Egbetokun daga mukamin Sufeton yan sandan Najeriya

Tinubu ya maye gurbin Egbetokun da Tunji Disu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami Kayode Egbetokun daga mukaminsa na Sufeto Janar na ‘yan Sanda (IGP).

Manyan jami’an ‘yan sanda da majiyoyi daga Hukumar Kula da Ayyukan ‘yan Sanda sun tabbatar da faruwar lamarin.

An sanar da cewa Tunji Disu, wanda ke rike da mukamin Mataimakin Sufeto Janar mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda (FCID) a Alagbon, Legas, shi ne zai gaji Egbetokun.

Wata majiya ta bayyana cewa, “Egbetokun ya je Fadar Shugaban Kasa jiya inda aka umarce shi da ya fara shirya takardun mika mulki. Da alama ya kammala hakan kuma zai mika ragamar aiki ga Tunji Disu.”

Majiyar ta kara da cewa an zargi tsohon IGP da gazawa da kuma amfani da iko fiye da kima, tare da cewa wa’adinsa ya fuskanci cece-kuce da dama.

Rahotanni sun ce an ba shi shawarar ya sauka domin mayar da hankali kan jinyar wata matsalar koda da yake fama da ita.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments