Hakan dai na kunshe ne cikin wani rahoto da kwamitin ya mika fadar White House kan bincike da shawarwari bisa zargin kisan Kiristoci a Najeriya.
Ɗan majalisa Riley Moore ne ya tabbatar da mika rahoton a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X.
Yace rahoton ya bayyana ne biyo bayan watanni da suka dauka suna bincike da sauraron ƙwararru da shaidun gani da ido da kuma tattaunawa da shugabannin addini yayin ziyarar gano gaskiya da suka kawo Najeriya.
Daga cikin shawarwarin da suka bayar a cikin rahoton har da bukatar a soke shari’ar Musulunci da dokokin ɓatanci ga Annabi SAW, sanya takunkumin biza ga mutanen ko kungiyoyin da ke da hannu a muzgunawa Kiristoci.
Mr. Moore ya yabawa Trump bisa sake sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ya kamata a sanya ido a kansu.