Yau ake cika shekaru 4 cif da faro yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine, wanda ke zuwa tun bayan da Moscow ta fara mamaya a maƙwabciyartata a ranar 24 ga watan Fabarairun 2022.
Gabanin fara wannan mamaya, tun da farko ƙasashen sun yi ta jita-jitar yiwuwar Rashar ta ƙaddamar da hare-hare kan Ukraine batun da Moscow ta riƙa musantawa a lokuta da dama.
Yunƙurin Ukraine na shiga ƙungiyar tsaro ta Nato da kuma zama mambar ƙungiyar Tarayyar Turai baya ga ƙaruwar kusancinta da ƙasashen yammaci musamman Amurka na daga cikin dalilan da suka haddasa wannan yaƙi.
Da fari, shugaba Vladimir Putin a ranar 24 ga watan Fabarairun 2022 ya sanar da faro atisayen Soji wanda ya ce manufa ce ta ƙwace makamai daga hannun ɓatagari akan iyakar ƙasashen biyu, da kuma kakkaɓe barazanar masu aƙidar Nazi.
Duk da cewa Putin ya yi iƙirarin cewa ba shi da nufin mamayar Ukraine, amma hare-haren dakarun nasa ya juye zuwa farmakar muhimman wurare a Kyiv ciki har da rukunin gidajen jama’a.
Cikin gaggawa ƙasashen duniya suka yi tir da matakin na Rasha tare da ƙaƙaba mata takunkuman karya tattalin arziƙi baya ga ƙunshin tallafi ga Ukraine don ta samu damar kare kanta.
Tun a watanni biyu da faro wannan Rasha ta kama hanyar ƙwace iko da Kyiv gabanin janyewar dakarunta bayan Ukraine ta samu tallafi daga ƙasashe da kuma sojojin hayar da ke tallafa mata.
A tsawon shekaru 4 da aka shafe ana wannan yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine, dukkanin ɓangarorin sun tafka asara mai tarin yawa kama daga ta dakaru waɗanda aka yi ittifaƙin sun haura dubu 57 da 500 baya ga wasu fiye da dubu 300 da suka jikkata sai kuma tarin dukiya mai tarin yawa da gwamnatocin ƙasashen biyu suka yi asara a wannan yaƙi.
Cikin watan Satumban shekarar ta 2022 ne Rasha ta sanar da ƙwace yankuna 4 na Ukraine da suka ƙunshi Donetsk da Luhansk da Zaporozhye da kuma Kherson matakin da ya gamu da kakkausar suka daga ƙasashen duniya.
Dama tun a shekarar 2014 Rashan ta ƙwace iko da yankunan Crimea da Sevastopol dukkaninsu waɗanda a baya ke matsayin mallakin Ukraine.