Rundunar Sojojin Najeriya ta gargadi dakarunta da ke gudanar da ayyuka a Jihar Zamfara da su kiyaye mutuncin fararen hula tare da kaucewa duk wani nau’i na cin zarafi yayin da suke aikin tsaro.
Rundunar ta bayar da gargaɗin ne a yayin wani gagarumin taro da ta shirya a Gusau, babban birnin jihar, inda ta jaddada buƙatar sojoji su riƙa aiki bisa tanadin doka da ƙa’idojin aikin soja.
A cewar rundunar, kare mutuncin fararen hula da bin dokokin aiki na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen kare martabar rundunar tare da ƙarfafa amincewar jama’a da ayyukan sojoji.
Rundunar Sojojin Najeriya dai ta nanata cewa za ta ɗauki mataki kan duk wani soja da aka samu da laifin tauye haƙƙin jama’a ko karya dokokin aikin tsaro.