Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAtiku ya yi ganawar sirri da Sen Abdul’aziz Yari

Atiku ya yi ganawar sirri da Sen Abdul’aziz Yari

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi wata ganawar sirri da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari, an Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ganawar sirrin ta gudana ne a gidan Atiku da ke Abuja,

Sai dai daga Atiku har Yari, babu wanda ya zanta da manema labarai bayan kammala ganawar.

Haka kuma ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan dalilin ganawar ba har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto.

Wannan lamari dai ya haifar da hasashe a fagen siyasa, musamman a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan haɗin kai da sauye-sauyen jam’iyu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments