Yan bindiga ɗauke da makamai sun cinna wuta a ofishin ’yan sanda a hedikwatar Ƙaramar Hukumar Agwara da ke Jihar Nejan Najeriya, inda suka yi garkuwa da wasu mutum shida da sanyin safiyar Lahadi.
Majiyoyi sun shaida cewa maharan sun isa yankin da misalin ƙarfe 4:00 na asuba, inda suka yi artabu da jami’an ’yan sanda da manyan makamai, lamarin da ya tilasta wa jami’an tserewa.
Bayan ƙona ofishin ’yan sanda, ƴan ta’addan sun nufi Cocin UMC tare da banka masa wuta, daga bisani suka tafi da mutum shida.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, bayan sun fice daga garin Agwara, maharan sun kai hari a yankin Sokonbara, inda suka kashe wata mata tare da kwashe kayan abinci.
Majiyoyi sun ce daga cikin waɗanda aka sace akwai tsohon Shugaban Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Ƙasar (NUT) na Ƙaramar Hukumar Agwara, Malam Ahmed Burade, tare da matarsa da ’ya’yansa huɗu.
Sai dai bayanai sun ce Malam Ahmed Burade ya tsere ne a yayin musayar wuta tsakanin ’yan ta’addan da ’yan sa-kai, amma matarsa wadda ke jinya da ’ya’yansu huɗu an tafi da su.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta bakin mai magana da yawunta, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar harin, sai dai ya ce ba a samu asarar rai ba.