Gwamnatin tarayya ta ce za ta ɗauki matakan gaggawa domin tallafa wa manoma bayan da farashin wasu kayan abinci ya faɗi warwas a kasuwa.
Gwamnatin ta bayyana shirin ta na tallafa wa manoman ƙasar nan bayan da aka lura cewa farashin wasu kayan abinci ya faɗi.
Ministan kuɗi, Wale Edun, ne ya bayyana haka yayin gabatar da jawabin bude taron ƙaddamar da rahoton hasashen tattalin arzikin 2026 na kungiyar NESG a Lagos
Rahotanni sun bayyana cewa ministan ya ce matakan tallafin za su kasance cikin gaggawa domin ƙarfafa manoma su ci gaba da zuba jari a noma, tare da kare nasarorin da aka samu na saukar farashin abinci a ƙasar.
A cewar Wale Edun, wasu farashin kayan abinci sun sauka ƙasa da kuɗin da manoma ke kashewa wajen samar da su, lamarin da zai iya hana su ci gaba da noma idan ba a ɗauki mataki ba.
Ya ce: “Akwai bukatar taimaka wa manoma a wannan lokaci, domin a wasu lokuta farashin ya faɗi ƙasa da kuɗin samarwa, kuma za a magance hakan cikin gaggawa domin ƙarfafa ci gaba da zuba jari a samar da abinci.”
Ministan dai ya jaddada cewa manufar gwamnati ita ce daidaita buƙatun masu saye da kuma ƙarfafa masu samarwa, musamman kananan manoma da ke da muhimmiyar rawa a wadatar abinci.