Saturday, October 17, 2026
HomeLabarai‘Yan sanda sun cafke wasu kayan fashewa da miyagun kwayoyi a Kano

‘Yan sanda sun cafke wasu kayan fashewa da miyagun kwayoyi a Kano

Rundunar yan sandan kano ta tabbatar da kama wasu miyagun kwayoyi da wasu abubuwan fashewa

Rundunar ‘Yan sandan Kano sun yi nasarar kama kayayyakin da ake zargin abubuwan fashewa ne tare da miyagun kwayoyi a wasu ayyuka biyu daban-daban da aka gudanar a sassa daban-daban na kananan hukumomin cikin birnin Kano.Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Juma’a.

Kiyawa ya bayyana cewa, a ranar Litinin, jami’an ‘yan sanda da ke aiki a Ofishin ‘Yan Sanda na Rijiyar Lemo, bisa umarnin Kwamishinan ‘Yan Sanda, sun aiwatar da bincike a wani gida da ke Unguwar Tudun Bojuwa, a Karamar Hukumar Fagge, inda suka gano manyan buhuna guda biyu dauke da kayayyakin da ake zargin masu hatsari ne.

Ya ce tawagar kwararru na rundunar sun gudanar da bincike da tantancewa domin gano ainihin kayayyakin da aka kama.

A cewarsa, daya daga cikin buhunan ya kunshi nade-naden igiyoyin tayar da bam guda shida, yayin da dayan buhun ke dauke da fakiti 20 na ganyayyaki busassu da ake zargin hodar iblis ce, tare da fakiti 220 na kwayoyin Exol.

Ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

SourcePunch
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments