Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKotu ta yi watsi da karar da Gwamnatin Tarayya a shigar a...

Kotu ta yi watsi da karar da Gwamnatin Tarayya a shigar a kan Natasha

Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja ta yi watsi da tuhumar laifin da gwamnatin tarayya ta shigar kan Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, lamarin da ya kawo karshen shari’ar da ta dauki hankalin jama’a a fadin kasa.

Kotun ta dauki matakin ne bayan Ofishin Babban Lauyan Tarayya ya janye karar ta hanyar mika takardar dakatar da shari’a, wanda yasa aka soke tuhumar batanci da sauran laifuka da ake tuhumar ta.

Shari’ar ta samo asali ne daga kalaman da ake zargin Sanatar ta yi a wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin, wanda ta haifar da muhawara a fadin kasa kan ‘yancin fadin albarkacin baki, da kuma iyakar ikon gwamnati wajen gurfanar da mutane a kotu.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments