An sake samun wasu sabbin hare-haren ƴan bindiga a sassan jihar Katsina dai-dai lokacin da ake jita-jitar cewa gwamnatin jihar na wani shirin sakin ɗimbin ƴan bindigar da ake tsare da su bayan kamasu a lokuta da dama, sakin da mahukuntan ke cewa na ƙarƙashin yarjejeniyar da aka ƙulla a shirin zaman lafiyar jihar.
Rahotanni sun ce ƴan bindigar sun kai hari kan wata tawagar masu zuwa bikin aure a ƙauyen Unguwar Nagunda da ke ƙaramar hukumar ƙanƙara inda suka kashe aƙalla mutane 2 daga cikin mahalarta bikin a daren Lahadin da ta gabata.
A cewar bayanai, baya ga kisan mutanen 2 ƴan bindigar sun kuma sace mutane 17 ciki har da amaryar da ake tsaka da bikinta, bayan jikkata wasu gommai, kodayake bayanai sun ce 8 daga cikin mutanen da ƴan bindigar suka sace sun kuɓuta tare da komawa ga ahalinsu a jiya Litinin.
Akwai kuma wani harin na daban da ƴan bindigar suka kashe mutum guda a ƙauyen Jaga na ƙaramar hukumar ƙanƙara.
Gabanin wannan sabbin hare-haren, ƴan bindigar an jiyo kwamishinan tsaron jihar ta Katsina Nasir Muazu na kare shirin gwamnatin jihar na sakin tarin ƴan bindigar da ke tsare da cewa manufa ce ta samar da zaman lafiya a jihar.
Aƙalla ƴan bindiga 70 ne ke fuskantar shari’a kan ayyukan ta’addanci za a saki, yayin da bayanai ke cewa gwamnatin jihar ta Katsina ke shirin saki don samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Sai dai a jiya Litinin, kwamishinan tsaron ya bayyana cewa babu cikakkun alƙaluman ƴan bindigar da za a saki ƙarƙashin shirin zaman lafiyar.