Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana kansa a matsayin muƙaddashin shugaban ƙasar Venezuela, kwanaki kaɗan bayan kai hari ƙasar inda aka kama Shugaba Nicolas Maduro da mai ɗakinsa aka tafi da su Amurka.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Shugaba Trump ya nuna kansa a matsayin muƙaddashin shugaban ƙasar da ke Kudancin Amurka daga watan Janairun 2026.
“Za a sayar da man da za mu karɓa daga Venezuela a farashin kasuwa, kuma ni da kaina, a matsayina na shugaban Amurka, zan riƙa juya ribar da aka samu,” a cewar Shugaban.