Guguwar tarzoma na ci gaba da ƙamari a ƙasar Iran, yayin da aka shiga kwana na 13 a jere.
Yanzu ana kallon tarzomar a matsayin tashin hankali mafi girma tun bayan tashe-tashen hankula a 2009.
Hukumomin ƙasar sun katse intanet tare da yanke hanyoyin sadarwa ta wayar tarho.
Haka kuma jami’an tsaro sun harba bindiga da kuma hayaƙi mai sa hawaye a kan wasu zanga-zangar.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar riƙe da kwalaye da ke ɗauke da saƙon nuna goyon baya ga tsohon Yerima mai jiran gado da ke gudun hijira, Reza Pahlavi.