Shugaba Trump ya yi gargaɗin cewa Amurka za ta iya sake kaddamar da hare-hare a Najeriya idan har a cewarsa aka ci gaba da kashe Kiristoci.
Trump ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Jaridar New York Times da aka wallafa a ranar Alhamis.
Gwamnatin Najeriya ta sha musanta ikirarin danganta kashe-kashen ƙasar da kisan Kiristoci kawai.
A cikin hirar da aka yi da Donald Trump, ya ce ya so ya kai hari ɗaya amma a cewarsa idan aka ci gaba da kisan kiristoci, Amurka za ta sake ƙaddamar da wasu hare-hare a Najeriya.
Ya kuma ce harin ranar Kirsimeti da Amurka ta kai a Najeriya na hadin guiwa ne da hukumomin ƙasar.
Sannan da aka yi masa batun da mai ba shi shawara kan harakokin Afrika kan tsokacinsa cewa ƴan ta’adda sun fi kisan musulmi fiye da kiristoci a Najeriya, sai trump ya amsa cewa ya yarda ana kisan musulmi a hare-haren na Najeriya amma a cewarsa an fi kisan kiritoci.
A karshen watan Oktoba ne Trump ya fara gargadin cewa kiristoci na fuskantar barazana tare da yi gargadin zai kai wa Najeriya hari kan abin da ya kira gamnati ta gaza wajen kare kiristoci, zargin da gwamnatin Najeriya ta musunta, tana mai cewa rikicin kasar ya shafi dukkanin bangarorin addini na ƙasar ba tare da fifita wani addini ba.