Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta fara gudanar da matakan tsige Gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.
Majalisar dai ta kaddamar da shirin tsige gwamnan ne a zaman ta na yau Alhamis.
‘Yan majalisar dai suna zargin Fubara da mataimakinsa da aikata mummunan laifi.
Kakakin majalisar, Martin Amaewhule, ne ke jagorantar zaman majalisar da aka fara aiwatar da wannan tsari.
Abubuwan da suka faru a zaman sun nuna sake kunno kai na rikicin siyasa tsakanin Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT).
A ranar 5 ga Disamba, 2025, ne dai wasu ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Rivers karkashin jagorancin kakakin majalisar suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Kwanaki kadan bayan haka, Gwamna Fubara ma ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC.
Sai dai kalaman barazana da maganganu masu nuna adawa a tsakanin, Wike da Fubara, sun ci gaba, lamarin da ya kai ga ayyana dokar ta-baci a jihar a watan Maris na shekarar 2025.