Wani sabon rahoto da aka fitar ya nuna cewa ‘yan Najeriya akalla miliyan 141 ne za su fada cikin kangin talauci a wannan shekarar.
Kamfanin binciken tattalin arziki na PwC ya fitar da rahoton, inda ya ce kashi 62 na al’ummar Najeriya, za su rasa arzikinsu, su fada talauci a 2026.
Rahoton ya yi nuni da cewa duk da matakan da gwamnati ke ɗauka na gyara tattalin arziki, wasu manyan dalilai za su jefa miliyoyin mutane a talauci.
A cewar kamfanin PwC, hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin ƙaruwar kuɗaɗen shiga za su ci gaba da jefa iyalai da dama cikin mawuyacin hali kafin zaɓen 2027.
Rahoton ya bayyana cewa talakawa a Najeriya na kashe kusan kashi 70 na dukkan kuɗaɗen shigarsu wajen sayen abinci kaɗai, wanda hakan ke barinsu cikin mawuyacin hali idan farashi ya ƙara tashi.
Duk da akwai hasashen da ake yi na cewa hauhawar farashin kaya zai ragu nan gaba kadan, amma rahoton ya jaddada cewa tsadar makamashi, sufuri, da kuma faduwar darajar Naira za su ci gaba da sa farashin abinci da sauran muhimman buƙatu zama masu wahalar samu ga talakan Najeriya.