‘Yan wasan Super Eagles sun yi barazanar cewa ba za su je Marrakech domin buga wasansu na gaba da kasar Algeria a gasar cin kofin ƙasashen nahiyar Afrika ta AFCON ba, sai dai idan har hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta biya dukkan kudaden alawus-alawus din da suka yi nasara.
A cewar majiyar, ‘yan wasan tare da jami’ai na ci gaba da jiran biyan su alawus-alawus daga gasar.
Bayanai sun nuna cewa har yanzu ba a cimma daidaito akan wannan lamarin alawus-alawus ɗin na wasanni hudu da suka kara da Tanzania da Tunisia da Uganda da kuma Mozambique ba.
Yayin da kungiyar ke ci gaba da jajircewa a gasar, sun bayyana karara cewa ba za su yi atisaye ko kuma su je Marrakech a wasa na gaba ba, sai dai in an warware batun kudaden da aka biya, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.
Idan za a tuna wa a watan Nuwamba, kungiyar ta yi irin wannan barazanar ta kauracewa wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za ta yi da Gabon a 2026, saboda rashin biyansu hakkokinsu.