Ƙasar Rasha ta sake yi wa Ukraine luguden hare-haren da manyan makamai a ciki dare.
Magajin garin Kyiv, Vitali Klitschko ya ce an kai wa gundumomi da dama na birnin hare-haren bama-bamai.
Mista Klitschko ya kuma ce harin ya shafi gidaje da wata cibiyar kasuwanci da kuma wani asibiti.
Magajin garin ya ƙara da cewa an kashe mutum huɗu, sannan wasu 19 suka jikkata.
A halin da ake ciki, hukumomi a yankin Lviv da ke yamacin ƙasar sun ce an lalata muhimman ababen more rayuwa da dama.