Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKiristoci sun gargadi Nyesom Wike kan rigimarsa da Gwamnan Bauchi

Kiristoci sun gargadi Nyesom Wike kan rigimarsa da Gwamnan Bauchi

Kungiyar farar hula mai suna Christian Youth in Politics (CYP), reshen Jihar Bauchi, ta gargadi Ministan Abuja, Barrista Nyesom Wike.

Kungiyar ta tura gargadin ne ga a jiya Talata 6 ga watan Disambar 2025, inda ta nemi Wike ya nisanci harkokin siyasar Jihar da rigima da Gwamna Bala Mohammed.

Sakataren kungiyar, Kwamred Ishemu Taimako Ibrahim, ya zargi ministan da katsalandan a siyasa.

Taimako ya ce yadda Nyesom Wike ke mu’amala da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi na haifar da damuwa kan kundin tsarin mulki da tafiyar dimokuradiyya.

A cewar kungiyar, Gwamna Bala ya riga ya koka kan fuskantar tsoratarwa da danniya ta siyasa, sakamakon amfani da ‘yancinsa na kundin tsarin mulki na shiga harkar siyasa, musamman kin sauya sheka zuwa APC.

Game da zargin amfani da EFCC da tsoratarwa, Taimako ya bayyana matukar damuwa kan batun, musamman Hukumar EFCC wajen tsoratarwa da gallaza wa Kwamishinan Kudi na Jihar Bauchi saboda dalilan siyasa, maimakon gudanar da bincike na gaskiya bisa hujjoji.

Kungiyar ta ce hakan ya saba wa ka’idojin adalci da dokar kasa, inda ta bukaci hukumomin tsaro da na bincike da su guji goyon bayan danniya ko ramuwar gayya ta siyasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments