Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya bawa mace ta farko mukamin shugabar makarantar horas da lauyoyi

Tinubu ya bawa mace ta farko mukamin shugabar makarantar horas da lauyoyi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Olugbemisola Odusote a matsayin sabuwar Shugaba ta makarantar horar da lauyoyi ta Najeriya.

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta ce naɗin zai fara aiki daga ranar 10 ga Janairu, 2026, kuma an tsara wa’adin ne na tsawon shekaru huɗu.

A matsayinta na Shugaba, Odusote za ta kasance mai jagorantar harkokin ilimi gaba ɗaya.

Haka kuma za ta kuma da tafiyar da harkokin gudanarwa, da kuma tsara alkiblar ci gaban makarantar a dukkan rassanta da ke faɗin ƙasar nan. Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa Odusote za ta zama babbar hanyar haɗin gwiwa tsakanin makarantar lauyoyi ta Najeriya.

Za kuma ta yi aiki da hukumar koyar da Ilimin lauya, Majalisar masu nada lauyoyi da kuma kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA).

Ana ganin wannan matsayi zai ba ta damar tabbatar da daidaito da ingancin horon lauyoyi a ƙasar da kuma inganta aikin lauya baki daya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments