Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta ceto yara huɗu da aka sace tare da mayar da su hannun iyalansu.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, SP Rahman Nansel, ya fitar a ranar Talata a birnin Lafia.
Sanarwar ta ce rundunar ta fara bincike ne bayan samun rahoton ɓacewar yaran a ranar 31 ga watan Disamba 2025 a sashen ’yan sanda na New Nyanya da ke Karamar Hukumar Karu.
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an bincike sun yi aiki tare da rundunar ’yan sanda ta Babban Birnin Tarayya, inda suka bi bayanan sirri zuwa wata maboyar masu laifi, sannan suka ceto yaran lafiya.
Rundunar ta bayyana cewa an riga an mayar da yaran ga iyalansu, yayin da ake ci gaba da farautar sauran mutanen da ake zargi da hannu a lamarin.