Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciAmurka ta hana ƴan Najeriya da wasu ƙasashe shiga ƙasar

Amurka ta hana ƴan Najeriya da wasu ƙasashe shiga ƙasar

Kasar Amurka ta sanya wa Najeriya da sauran wasu kasashen takunkumin shiga kasar

Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump ta sanar da sanya sabbin takunkuman hana shiga ƙasar, inda matakin ya shafi wasu ƙasashe ciki har da Najeriya saboda matsalar tsaro.

Takunkumin ya haɗa da haramta shigar ‘yan ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da Sudan ta Kudu, tare da mutanen da ke riƙe da takardun hukumomin Falasɗinawa.

Fadar White House ta ce an ɗauki matakin ne domin kare tsaron ƙasar da kuma tabbatar da kariya ga al’ummar Amurka.

Haka kuma, gwamnatin ta sanar da ƙwarya-ƙwaryar dakatar da tafiye-tafiye daga ƙasashe 15 ciki har da Najeriya, inda ta danganta matakin da barazanar tsaro da ayyukan ƙungiyar Boko Haram.

Ƙasashen Laos da Saliyo, waɗanda a baya aka sanya musu ƙwarya-ƙwaryar takunkumi, yanzu an tsaurara musu matakin inda aka dakatar da shigar ‘yan ƙasashensu gaba ɗaya.

Sabon takunkumin zai fara aiki ne daga watan Janairun 2026.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments