Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeTrump ya hana tankokin dakon mai shiga ko fita daga Venezuela

Trump ya hana tankokin dakon mai shiga ko fita daga Venezuela

Trump ya ba da umarnin dakatar da tankokin dokon mai shiga da fita Venezuela.

Shugaba Trump ya ce ya bayar da umarnin a dakatar da dukkan tankokin dakon mai daga shiga ko fita daga Venezuela, matakin da zai kara matsawa gwamnatin shugabanbin Nicolas Maduro lamba.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya ce sun ƙara yawan sojojin Amurka, a kusa da Venezeula.

Trump ya ce gwamnatin Maduro na ɗaukar nauyin ayyukan da suka shafi safarar ƙwayoyi da ta’addanci da safarar mutane da kisa da kuma satar mutane daga filyen man da ta sace.

Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki bayan da dakarun Amurka suka ƙwace wata motar dakon mai a yankin Karebiya tare da sanyawa wasu motocin shida takunkumi wani yunkuri da ya ce zai shafi hanyar kudin shigar kasar.

Tuni dai gwamnatin Venezuela ta yi Allah-wadai da matakin Trump din tana mai cewa ya take hakkin kasuwanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments