Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKotu ta yanke wa wasu yan Najeriya 4 hukuncin kisa

Kotu ta yanke wa wasu yan Najeriya 4 hukuncin kisa

Wata babbar kotun jihar Akwa Ibom da ke zamanta a Uyo ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da laifin garkuwa da mutane.

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun yi garkuwa da wani tsohon ma’aikacin kamfanin ExxonMobil, Idongesit Demas Udom, tare da yanke masa hannu bayan karɓar kudin fansa N5m.

Alkali ya ce lauyoyin gwamnati sun tabbatar da laifin wadanda ake tuhuma, yayin da aka wanke wasu uku saboda rashin hujjoji.

Tun da fari dai, shaidu sun fadawa kotu yadda wadanda aka yankewa hukunci suka sace tsohon ma’aikacin, suka karbi kudin fansa N5m

Kotu ta same su da laifuffuka guda uku da suka hada da haɗin baki, garkuwa da mutum, da kuma yi wa wani rauni da gangan domin nakasa shi.

Mai shari’a Gabriel Ette ne ya yanke hukuncin bayan karanta shari’ar tsawon kusan awa hudu, inda ya ce ɓangaren masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin waɗanda ake tuhuma.

Sai dai kotu ta sallami tare da wanke mutane uku – Kingsley John Akpan (32); Etimefiok Ime Ezekiel (37); da Joseph Sunday Etim (31) – sakamakon rashin isassun hujjojin da ke danganta su da laifin.

A yayin yanke hukunci, mai shari’a Ette ya yanke wa kowane ɗan laifi hukuncin daurin shekaru bakwai kan haɗin baki, hukuncin kisa ta hanyar rataya kan garkuwa da mutum, da kuma daurin shekaru uku kan raunatawa da gangan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments