Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamna Abba ya dauki sabon mataki kan matsalar tsaro

Gwamna Abba ya dauki sabon mataki kan matsalar tsaro

Abba Kabir Yusuf ya amince da kafa wata sabuwar runduna ta musamman wadda za ta rika sanya idanu a tashoshin motar da ake da su.


Gwamna Abba Kabir ya amince da kafa rundunar ne domin tunkarar matsalolin tsaro a tashoshin mota da sauran muhimman wuraren taruwar jama’a a fadin jihar Kano.

Rundunar za kuma ta yi aikin hadin gwiwa tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da kawar da aikata laifuffuka a fadin jihar

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, 14 ga watan Disamban 2025.

Meyasa aka kafa sabuwar rundunar?

A cewar sanarwar, wannan shiri mataki ne na rigakafi da nufin dakile barazanar tsaro tun kafin ta ta’azzara, karfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, da kuma dawo da amincewar jama’a.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada matsayar gwamnatinsa ta rashin amincewa da aikta laifuffuka, tare da ba da tabbacin cikakken goyon baya ga hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

An bayyana tashoshin mota a matsayin wuraren da ke da haɗari sosai saboda yawan zirga-zirgar jama’a, da kuma wasu sababbin abubuwan da suka shafi tsaro, ciki har da kama wasu da ake zargi da aikata laifi a tashar mota ta Kofar Ruwa.

Sanarwar ta ce rundunar ta musamman za ta gudanar da tsauraran sintiri, tattara bayanan sirri, da hadin gwiwar ayyukan tsaro a tashoshin mota da sauran wuraren da ke da rauni.

Runduar za ta rika sa ido a gidajen mai haka kuma, aikin rundunar zai shafi gidajen mai da sauran wuraren taruwar jama’a inda ake yawan haduwa da cunkoso.

Wannan mataki dai ya nuna kudurin gwamnan Kano na hana aikata laifuffuka da kuma tabbatar da tsaron jihar Kano, musamman a manyan hanyoyin shiga da fita cikin birnin Kano.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments