Matawalle, wanda tsohon gwamna ne a Zamfara ya kare kansa game da zarge-zargen inda ya kalubalanci masu yaɗa hakan.
Hakan dai na cikin wani faifan bidiyo da DCL Hausa ta wallafa a Facebook yayin hira da tsohon gwamna.
A cikin bidiyon, Matawalle ya ce duk wani zargi da zai tabbata ba, bai zama zargi sai an je kotu an yi shari’a kafin sanin gaskiya.
Ya ce zargi ba ya zama gaskiya sai kotu ta tabbatar, yana gargadin cewa duk wanda ya bata masa suna ba tare da hujja ba zai fuskanci hukunci.
Ya bukaci duk mai zarginsa kan alaka da ta’addanci ya garzaya kotu da hujjoji domin gano gaskiyar lamarin.
Ya kara da cewa:
“Duk wani zargi da tabbatar da shi ba, ba gaskiya ba ne, duk mai zargi na ya je kotu.”
“Idan aka tabbatar abin da ya fada a kaina ba gaskiya ba ne, to duk abin da na nema na bata suna sai ya biya.”