Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce ayyukan Rwanda a Gabashin Dimokuraɗiyyar Congo ya saɓa wa yarjejeniyar zaman lafiya da Shugaba Donald Trump ya ƙulla tsakaninsu.
Ya ƙara da cewa za a ɗauki matakan ganin ɓangarorin sun ci gaba da mutunta tanade-tanaden yarjejeniyar.
A gefe guda kuma, Rwanda ta ce Congo ta yi watsi da yarjejeniyar saboda yadda take yunƙurin ƙwato wani yanki da ‘yan tawayen M23 suka kama.
Sai dai Ministan Harkokin wajen Rwanda Olivier Nduhungirehe ya bayyana mamakin zargin ƙasarsa da haddasa ci gaban faɗan.
‘Yan tawayen na M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun ƙwace gari na biyu mafi girma a yankin Kudancin Kivu mai maƙwabtaka da ƙasar Burundi.