Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeHarin Rasha: Sama da gidaje miliyan ɗaya sun rasa wutar lantarki a...

Harin Rasha: Sama da gidaje miliyan ɗaya sun rasa wutar lantarki a Ukraine

Gidaje sama da miliyan ɗaya ne ba su da wutar lantarki a Ukraine bayan wani ƙazamin harin da Rasha ta kai cikin dare.

Ministan harkokin cikin gida na Ukraine Ihor Klymenko, ya ce lamarin ya shafi yankuna biyar, yayin da aƙalla mutane biyar suka jikkata, kuma ana ci gaba da aikin kashe gobarar da ta tashi sakamakon harin.

Hare-haren Rasha kan ababen more rayuwa na makamashin Ukraine ya zama ruwan dare tun lokacin da aka fara yaƙin.

Moscow ta ƙara zafafa kai hare-hare yayin da ƙasar ke shiga lokacin hunturu.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wakilin shugaban Amurka Donald Trump a ƙasashen ƙetare zai je Jamus a ƙarshen wannan makon domin ganawa da shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky da shugabannin ƙasashen Turai domin tattaunawa kan kawo ƙarshen yaƙin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments