Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kare matakin da ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar Accord, yana mai cewa ya sauya sheƙa ne domin kare kansa da kuma tabbatar da zaman lafiyar jihar.
A hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, Adeleke ya ce bai yi watsi da PDP ba, wacce har yanzu ya ke girmamawa, sai dai ya zaɓi fifita ɗorewar ci gaban jihar Osun.
Ya ce: “Ba gaskiya ba ne cewa na yi watsi da PDP, ina son PDP, amma dole ne in kare kaina. Dole ne na tabbatar na kare jiha ta saboda kyawawan ayyukan da muke yi domin mu ci gaba.”
Adeleke ya shiga jam’iyyar Accord ne a ranar Talata bayan ya fice daga PDP, jam’iyyar da ta kai shi mulki a zaɓen gwamnan jihar na 2022.
A ranar Laraba ne ya samu tikitin takarar gwamna a karkashin sabon jam’iyyarsa ta Accord.
Yanzu haka zai kara da ‘yan takara da ‘yan jam’iyyar APC, PDP, da kuma jam’iyyar haɗaka ta ADC a zaben da ake sa ran zai kasance mai matukar tasiri ga makomar siyasarsa.