Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamna Abba kabir Yusuf ya yaba wa Dangote kan ware 25% na...

Gwamna Abba kabir Yusuf ya yaba wa Dangote kan ware 25% na dukiyarsa ga ayyukan jin kai

Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa Aliko Dangote bisa ware kashi 25% na dukiyarsa domin ayyukan jin kai.

Yayin da gidauniyar Dangote ta kaddamar da tallafin ilimi ga yaran da ba sa zuwa makaranta a Kano da sauran jihohi, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa Alhaji Aliko Dangote bisa keɓe kashi 25 cikin 100 na dukiyarsa domin ayyukan jin kai.

Yabon na Gwamnan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wani taro da aka gudanar a Eko Hotels, da ke Lagos, wanda ya samu halartar fitattun shugabanni na ƙasa, ciki har da mataimakin Shugaban Ƙasa, Gwamnonin Kano, Gombe, Nasarawa da Borno da kuma ministocin ilimi biyu.

A wajen taron, gidauniyar Aliko Dangote ta sanar da shirin tallafin ilimi na Naira biliyan 100 da zai kai ga dalibai 155,000 a fadin Najeriya.

Haka kuma ya jaddada cewa ana ci gaba da gudanar da bincike a fadin jihar domin gano adadin yaran da ba sa zuwa makaranta tare da ɗaukar matakan haɗa makarantun allo cikin tsarin koyarwa na zamani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments