Venezuela ta zargi Amurka da sata karara da kuma fashin teku bayan da dakarun Amurka suka kwace wani jirgin ruwa na dakon mai a gabar tekun kasarta.
Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce matakin wani shiri ne na lalata arzikin makamashi na Venezuela da gangan.
Sai dai jami’an Amurka sun ce jirgin ruwan yana safarar man da aka sanya takunkumin sayar da shi ne zuwa Iran kuma ana taimaka wa kungiyoyin ta’addanci da kudin da ake samu a cinikin.
Lamarin ya kasance ƙarin wata sabuwar dambarwa ta matsin lambar da Amurka ke yi wa shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro.
Mai dai shi ne babbar hanyar samun kudade na kasar ta Venezuela.