Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHukumar Alhazai ta Kano ta rufe karbar kudin ajiyar kujerar aikin hajjin...

Hukumar Alhazai ta Kano ta rufe karbar kudin ajiyar kujerar aikin hajjin 2026

Hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar takardun biyan kuɗin ajiyar kujerun aikin hajjin 2026.

Darakta Janar na hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbaffa, ya ce wa’adin karɓar kuɗin ya ƙare ne a ranar Juma’a, 5 ga Disamba 2025.

Ya bayyana cewa bayan kammala taron da aka gudanar da hukumar hajji ta Ƙasa NAHCON an Abuja ranar Alhamis din da ta gabata, babu wani ƙarin wa’adi da aka bayar dangane da biyan kuɗin.

Alhaji Lamin Rabi’u Danbaffa ya ce rufe karɓan kuɗin da wuri ya zama dole sakamakon sabon tsari da ƙa’idojin da hukumomin Saudiyya suka gabatar na aikin hajjin 2026.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi, ya fitar, an bayyana cewa sabbin dokokin sun buƙaci tsauraran matakan bin ƙa’ida da kammala shirye-shiryen gudanarwa tun da wuri domin samar da ingantaccen shiri ga maniyyata.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin gudanarwa, Alhaji Yusuf Lawan, ya gode wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa haɗin kan da suka nuna, tare da kira ga maniyyatan da su cika sharudda su yi haƙuri yayin da hukumar ke ci gaba da gudanar da matakai na gaba na shirye-shiryen tafiya.

SourcePrymid FM
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments