An sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar 4 ga watan Disamba, 2025 a birnin Washington.
A cikin wata sanarwar da ta fitar a shafinta na X, ma’aikatar harkokin wajen Rwanda ta ce Jamhuriyar Congo da Burundi ne suka fara takalarta ta hanyar amfani da jiragen yaƙi da kuma jirage marasa matuƙa wajen jefa bama-bamai a kan ƙauyuƙan da ke kusa da iyakarta, lamarin da ya tilasta wa mayaƙan M23 mayar da martani.
Rwanda dai ta yi wannan zargi ne bayan da mayaƙan da take marawa baya suka kutsa cikin Uvira a jiya Talata, birnin da shi ne na ƙarshe da ya rage a ƙarƙashin ikon gwamnatin Jamhuriyar Congo a yankin gabashin ƙasar.
Ya zuwa yanzu, fiye da mutane 200,000, daga ciki har da sojojin Jamhuriyar ta Congo sun tsere daga birnin Uvira zuwa cikin Burundi, duk da cewa jami’an gwamnatin yankin sun musanta rahotannin da ke cewa mayaƙan M23 sun ƙwace iko da birnin.
Tun a jiya Talata Amurka da ƙasashen Yammacin Turai da dama suka fitar da sanarwar haɗin gwiwa da ta buƙaci Rwanda ta gaggauta dakatar da sabon farmakin da mayaƙan M23 suka ƙaddamar.