An yi ‘yar hayaniya a yayin da ake tantance Emmanuel Adeyemi, tsohon ɗan takara daga jihar Ekiti da Tinubu ya nemi a tantance shi a matsayin jakada.
Ƙungiyar kwamitin harkokin ƙasashen waje ta nuna damuwa da wannan kuskuren, ta ce ya kamata wanda aka aika sunansa a matsayin jakada ya zama yana da ƙwarewa.
Wannan ya sa aka tsaya cak, har wani daga cikin tawagarsa ya fara neman sunan a intanet, lamarin da ya fusata kwamitin matuka.
Sanata Asuquo Ekpenyong ya ce irin wannan rashin sanin muhimman bayanai abin damuwa ne, musamman ga wanda zai wakilci Najeriya a ƙasashen waje.
Majalisar dattawa dai na ci gaba da tantance mutane 65 da Shugaba Tinubu ya aika mata domin mukaman jakadanci a fadin duniya bayan an shafe shekaru babu wakilci.