Shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta tabbatar da sunayen wasu mutane biyu domin nada su a matsayin kwamishinonin Hukumar Kula da Lantarki ta Najeriya (NERC).
Amma a takardar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta, babu sunan shugaban hukumar da Tinubu ya nada a baya, Injiniya Abdulahi Ramat.
Tinubu ya nemi a tabbatar da mutane biyu – Aisha Mahmoud Kanti-Bello da Fouad Animashaun, kamar yadda dokar lantarki ta 2023 ta tanada.
Tinubu ya bayyana cewa wannan sabuwar bukata ta maye gurbin takardar da ya aika tun ranar 6 ga Agusta, 2025, wacce ta kunshi sunan Ramat a matsayin shugaban hukumar.
Ramat ya taba zuwa hedikwatar NERC da magoya bayansa bayan sanar da nadinsa, sakamakon ritayar tsohon shugaban hukumar, Garba Usman ya yi.
Rikici ya kunno kai lokacin da mai ba shugaban kasa shawara, Bayo Onanuga, ya ce Ramat ya fara aiki nan take a matsayin mai rikon kwarya, daga baya kuma ya janye maganarsa, yana cewa sai an tabbatar da shi a Majalisar Dattawa.
Zanga-zanga kan jinkirin tabbatar da Ramat
Bayan watanni sun shude ba tare da tabbatar da Abdullahi Ramat ba, wasu matasa da ke goyon bayansa sun yi zanga-zanga a Majalisar Tarayya domin neman a amince da shi.
Shugabannin zanga-zangar sun ce babu hujjar majalisar dattawa ta jinkirta, tunda an riga an tantance shi kuma an ba da shawarar tabbatar da shi daga kwamitin wutar lantarki na majalisar.
Wata kungiya daga Kano ta zargi Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da kokarin hana a tabbatar da Ramat, har ma suna zargin cin hancin dala miliyan 10 — zargin da majalisar ta musanta sosai.
Kakakin majalisar dattawa, Yemi Adaramodu, ya ce an dakatar da tantancewar Ramat ne saboda “korafe-korafen jama’a masu tsanani,” ba saboda siyasa ko cin hanci ba.
Daga baya, wanda ya yi zargin, Alwan Hassan, ya nemi afuwa, ya ce zargin da ya yi wa Shugabannin Majalisar ba gaskiya ba ne kuma bai dace ba.
Dalilin da ya jawo tsaikon tabbatar da Ramat
Majiyoyi sun ce Ibrahim Masar, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, ne ya ba da sunan Ramat — ba tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje, kamar yadda ake yadawa.
Sun kara da cewa Ramat ya jefa kansa cikin matsala lokacin da ya yi gaggawar kokarin shiga ofis ba tare da an tabbatar da shi ba, tare da tasirin rikicin siyasa a Kano.
A cewar wasu, takaddama tsakanin Barau da Ganduje kan jagorancin APC a Kano ta taka rawa wurin hana tabbatar da Ramat.
Tun bayan ritayar tsohon shugaban hukumar Usman, Mataimakin Shugaban NERC, Dr. Musiliu Oseni, ke rike da ofishin a matsayin mai rikon kwarya, duk da cewa wa’adinsa ya kare a ranar 4 ga Disamba.
Rahotanni sun ce fadar shugaban kasa na shirin tura sunan Oseni zuwa Majalisar Dattawa domin nada shi sabon shugaban hukumar.