Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroTinubu ya rantsar da Christopher Musa a matsayin ministan tsaro

Tinubu ya rantsar da Christopher Musa a matsayin ministan tsaro

Majalisa ta tabbatar da nadin Musa bayan tsauraran tambayoyi kan matsalolin tsaro

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin sabon ministan tsaro.

Janar Musa mai ritaya ya isa fadar shugaban kasa da misalin ƙarfe 3:47 na rana, inda aka raka shi zuwa ofishin Bola Tinubu.

Tsohon shugaban rundunar tsaro na kasa (CDS) ya sha rantsuwar ofis a ranar Alhamis a fadar gwamnati da ke Abuja.

An rantsar da shi bayan majalisar dattawa ta tabbatar da nadinsa a ranar Laraba bayan tsawon sa’o’i biyar ana tantance shi.

A yayin zaman, an yi wa tsohon babban hafsan tsaron tambayoyi masu tsauri game da batutuwa da dama, daga ciki har da janye sojoji daga Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Maga a Jihar Kebbi, kafin sace dalibai a ranar 17 ga Nuwamba.

Ya shaida wa ‘yan majalisa cewa zai gaggauta kaddamar da cikakken bincike kan janye sojojin da zarar ya kama aiki.

Sabon Ministan ya kuma yi alƙawarin binciko kisan kwamandan runduna, Birgediya Janar Musa Uba, a Jihar Borno, tare da sauran hare-haren da suka shafi manyan jami’an soja.

Nadin Christopher Musa ya biyo bayan murabus da tsohon ministan tsaro, Mohammed Badaru ya yi bisa dalilan lafiya.

Kafin nadinsa, shi ne tsohon kwamandan ‘Operation Hadin Kai’ ne a Arewa maso Gabas, sannan ya jagoranci rundunar tsaro ta kasa, inda ya kula da haɗin gwiwar yaƙi da Boko Haram/ISWAP da ‘yan bindiga, kafin ya yi ritaya a watan Oktoba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments