Ministan Tsaro mai jiran rantsuwa, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa idan har ya shiga ofis, dole ne a daina tattaunawa da kuma biyan kuɗin fansa ga ‘yan bindiga a Najeriya.
Janar Musa ya yi wannan bayani ne jiya yayin tantance shi a gaban Majalisar Dattawa, inda ya ce yaƙi da rashin tsaro ba zai inganta gaba ɗaya ba har sai an samar da cikakkiyar rumbun bayanan ƴan ƙasa tare da danganta su da tsaro da banki da tsarin tantance mutum.
Tantancewar janar Musa ta zo ne a rana ɗaya da Majalisar Wakilai ta nemi a tabbatar da gudanar da shari’o’in ta’addanci a fili domin rage yawaitar laifukan ta’addanci da tashin hankali a ƙasar.
Yayin jawabinsa, Janar Musa ya tsaya tsayin daka cewa dole gwamnatoci su guji duk wani nau’i na tattaunawa da masu aikata ta’addanci, domin hakan na ƙara musu ƙarfi ne kawai.