Atiku Abubakar ya soki nadin da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa tsohon shugaban INEC, Mahmood Yakubu, a matsayin jakada.
Ya ce da shi ne shugaban ƙasa, babu abin da zai sa ya yi wa wanda ya jagoranci babban zaɓen da aka yi ta cece-kuce naɗi.
Atiku ya yi gargadin cewa wannan mataki na iya zama kamar lada ne ba bisa cancanta ba, kuma hakan zai iya lalata martabar zaben Najeriya.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku, ya ce wannan mataki ba wani abu ne da zai taɓa yi ba idan shi ne shugaban ƙasa.
A cewar Atiku, wannan abu da Shugaba Bola Tinubu ya yi, za a iya fassara shi a matsayin bayar da lada, amma ba wai an yi naɗin saboda cancanta ba.
Ya ƙara da cewa tun da gwamnatin Tinubu na fama da matsalolin sahihancin ta fuskoki da dama, bai kamata ta ƙara ɗora kanta a irin wannan zargi ba.