An fara samun sabani tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin Rivers bayan wata biyu da dawo da tsarin dimokuradiyya.
Majalisar ta zargi gwamnatin Fubara da watsi da makarantu tare da tambayar yadda aka yi da N600bn da aka bari a baitul-malin jihar. Gwamna Simi Fubara ya mayar da martani cewa ba zai dauki ma’aikata don biyan bukatun siyasa ba, sai dai bisa bukatar jihar kawai.