Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa na neman amincewa da sabon bashin waje.
Buƙatar ta ƙunshi rancen Dala biliyan 20.52 da kuma Yuro biliyan 1.05, wanda ya janyo muhawara kan yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da bashin ƙasar.
Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da rashin bayyana cikakkun bayanai kan ayyukan da za a gudanar da kuɗaɗen, wuraren da za a aiwatar da ayyukan, da kuma tsarin biyan bashin.
Saboda haka, ya buƙaci Majalisar Tarayya da kada ta amince da buƙatar har sai gwamnati ta gabatar da cikakken bayani kan ayyukan da za a kashe kuɗaɗen a kansu.
Matsayar Atiku na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan manufofin rance na gwamnatin tarayya da kuma tasirin bashin ƙasa ga tattalin arzikin Najeriya.